Kotun koli: PDP ta taya Gwamna Wike murnar samun nasara

Kotun koli: PDP ta taya Gwamna Wike murnar samun nasara

-PDP ta taya Gwamna Nyesom Wike na jihar Rivers murnar samun nasara a Kotun kolin Najeriya

-Festus Awara na jam'iyyar AAC ne ya shigar da karar inda yake kalubalantar nasarar Wike a zaben gwamnan jihar da ya gabata

Kotun koli ta tabbatar da nasarar Gwamna Nyesom Wike na jihar Rivers inda ta yi watsi da korafin Awara Festus da jam’iyyarsa ta African Action Congress (AAC).

Kwamitin alkalai guda bakwai ne suka yanke wannan hukuncin inda suka tabbatar da abinda kotun sauraron karar zaben ta yanke.

KU KARANTA:Satar yara 9: Ganduje ya kafa kwamitin bincike game da lamarin

Tun a kotun zaben, alkali yayi watsi da korafin Festus da jam’iyyarsa ta AAC. Hakan bai sa dan takarar ya hakura sai ya zarce zuwa kotu ta gaba domin daukaka karar.

Zuwansa kotun daukaka karar ya haife masa da mai ido kasancewar kotun ta soke hukuncin kotun zaben, inda ta ce watsi da kararsa sam bai kamata ba.

A karshe dai Kotun kolin Najeriya ce ta raba gardama a tsakanin Wike na jam’iyyar PDP da Festus na AAC, inda ta tabbatarwa Wike da nasara ta hanyar yin watsi da korafin Festus ga baki dayansa.

A bangare guda kuwa, mai magana da yawun bakin PDP, Kola Ologbondiyan, ya jinjinawa Kotun koli bisa wannan shari’ar inda ya ce tayi abinda ya dace.

A cewarsa yanzu ne al’ummar Najeriya za su kara sanin muhimmancin kotun kasancewar an kwatanta adalci yayin zartar da hukunci, kuma ya taya Gwamna Wike murnar wannan babbar nasara da ya samu.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel