Satar yara 9: Ganduje ya kafa kwamitin bincike game da lamarin

Satar yara 9: Ganduje ya kafa kwamitin bincike game da lamarin

-Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya kafa kwamitin binciken sace-sacen yara a Kano

-Kwamitin zai gudanar da aikinsa ne tun daga kan yaran da aka sace a shekarar 2010 zuwa yanzu

-Satar wadansu yara 9 'yan asalin jihar Kano wadanda aka gano a Onitsha ne ya sanya Gwamnan kafa wannan kwamiti

Gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya kafa wani kwamitin domin binciken yadda aka sace wadansu yara tara da aka sace daga jihar Kano zuwa Onitsha ta Anambra.

Jastis Wada Umar Rano shi ne zai jagoranci kwamitin inda aka daura masu alhakin samo bayani game da sauran yaran da suka bace.

KU KARANTA:Gwamnan APC ya kai ziyarar ba zata asibiti da makaranta a jiharsa

Kwamitin zai yi bincike ne a akan dukkanin yaran da aka taba sacewa a Kano daga shekarar 2010 zuwa yanzu. Duk wani bayanin da zai taimaka game da sanin abinda ya faru da sace-sacen yaran shi ake bukata.

Har ila yau, daga cikin tsarin aikin kwamitin doka ta tabbatar masu da kira duk wani mutum dake a ciki ko wajen Najeriya domin ya bada shaidu a rubuce ko da baki game da wannan al’amari.

A wani labarin kuwa, za ku ji cewa Abdullahi Umar Ganduje na Kano ya soma raba kayan makaranta da littafan karatu ga daliban makarantun firamare a Kano.

Gwamna Ganduje ya fara raba kayan ne a wata makarantar firamare dake karamar hukumar Kumbotso, a ranar Alhamis 24 ga watan Oktoba. Inda ya ce wannan shirin zai zagaya kananan hukumomin jihar guda 44.

https://punchng.com/ganduje-institutes-panel-to-probe-kidnap-of-nine-kano-kids/amp/?__twitter_impression=true

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel