'Yan bindiga 210 ne suka mika makamansu tare da sakin wadanda sukayi garkuwa dasu a Sokoto

'Yan bindiga 210 ne suka mika makamansu tare da sakin wadanda sukayi garkuwa dasu a Sokoto

- A kalla 'yan bindiga 210 ne suka mika makamansu tare da sakin duk mutanen da suka yi garkuwa dasu

- Hakan kuwa ya biyo bayan sulhun da suka yi da gwamnatin jihar Sokoto

- Ita kuwa gwamnatin tuni da fara aiyukan farfado da yankunan 'yan bindigar don cika alkawarin da suka dauka

A kalla 'yan bindiga 210 ne suka mika makamansu tare da sakin mutanen da suka yi garkuwa dasu a jihar Sokoto, in ji kwamishinan tsaro na jihar.

Col garba Moyi mai murabus, ya bayyana hakan a Sokoto yayin tofa albarkacin bakinsa akan makamai 102 da aka karba daga 'yan bindigar bayan sulhun da suka yi da gwamnatin jihar.

KU KARANTA: Safiyya Ahmad, ta lashe gasar Hikayata na bana

Ya yi bayanin cewa, kungiyoyi 7 na 'yan bindigar ne masu mambobi akalla 30 suka mika makamai.

"Sun saki wadanda suka yi garkuwa dasu fiye da mutane 30 har da 'yan jihohin Zamfara da Kebbi. munat tattaunawa dasu na tsawon lokaci kuma munyi yarjejeniya dasu. Yarjejeniyar itace ta sakin wadanda suka sace,"

"A watanni kusan uku da suka gabat, basu sace kowa ba kuma babu kauyen da suka kaiwa hari kamar yadda suke yi. duk kashe-kashen da suke yi sun dena. Wannan na daga cikin yarjejejiniyar," Moyi ya sanar.

Moyi yace, daga bangaren gwamnatin jihar kuma, sun amince zasu kai wasu aiyukan cigaba yankunasu. A halin yanzu an fara wasu manyan aiyukan a yankuna da suka hada da gina ruga, haka burtsatse, hanyar wucewar shanu da sauransu.

kamar yadda yace, su kuma 'yan ta'addan suna ta aje makamansu wanda hakan na da matukar muhimmanci.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel