Kuma dai, Yan sanda sun sake ceto yara 2 daga hannun masu safarar mutane a Anambra

Kuma dai, Yan sanda sun sake ceto yara 2 daga hannun masu safarar mutane a Anambra

'Yan sanda sun kama mata uku kan laifin satar kananan yara biyu a garin Nkpor a karamar hukumar Idemili ta Arewa na jihar Anambra.

An kama wadanda ake zargin ne a mahadar kasuwar Nkpor/Tarzan tare da yaran biyu da suka sato kuma sun gaza bayar da gamsashen bayani kan inda za su tafi da yaran.

The Nation ta ruwaito cewa yaran biyu duk maza ne masu shekaru tsakanin biyu zuwa hudu.

Mai magana da yawun 'yan sandan jihar, Haruna Mohammed ya tabbatar da kamen da aka yi.

Kuma dai, Yan sanda sun sake ceto yara 2 daga hannun masa safarar mutane a Anambra
Kuma dai, Yan sanda sun sake ceto yara 2 daga hannun masa safarar mutane a Anambra
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Ban iya magana da harshen hausa sosai ba - Zahra Buhari

Ya ce, "Bayan samun bayyanan sirri, jami'an 'yan sanda ta CMU a jihar Anambra sun kama mata uku da ake zargi a kusa da mahadar kasuwar Nkpor/Tarzan a karamar hukumar Indemili ta jihar Anambra.

"An kama wadanda ake zargin dauke da kananan yara biyu wanda shekarun su bai wuce biyu zuwa hudu ba.

"Sun kasa bayar da gamsashen bayani a kan yaran ko kuma inda suke dauko yaran."

Mohammed ya kara da cewa ana zurfafa bincike kan lamarin kuma daga bisani za a gurfanar da wadanda ake zargi a gaban kuliya.

Ya kara da cewa, "Kwamishinan 'yan sandan jihar, Johan Abang ya bukaci iyayen da 'ya'yan su suka bace su garzaya zuwa hedkwatan rundunar da ke Akwa don su bincike ko 'ya'yansu ne sannan su karbe su."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel