Yanzu -Yanzu: An sako dalibai da malaman da akayi garkuwa dasu a jihar Kaduna

Yanzu -Yanzu: An sako dalibai da malaman da akayi garkuwa dasu a jihar Kaduna

- Masu garkuwa da mutane sun sako dalibai da malaman jihar kaduna da suka yi garkuwa dasu

- Mai magana da yawun gwamnan jihar, Samuel Aruwan ne ya bayyana hakan ga manema labarai a yau Asabar

- Gwamnatin jihar Kaduna ta hori jama'ar jihar da jami'an tsaro dasu bada hadin kai don ganin kawo kasrhen kalubalen tsaro dake addabar jihar

Masu garkuwa da mutane da suka sace dalibai da malaman makarantar Engravers College a Kaduna sun sakosu.

Mai magana da yawun gwamnatin jihar Kaduna, Samuel Aruwan ne ya bayyana hakan ga wakilin TVC a Kaduna. Ya bayyana cewa, an sako daliban da malaman ne a yau Asabar.

KU KARANTA: Tsoffin tsagerun Niger Delta sun yi barazanar komawa ruwa, sun bada sharadi

Gwamnatin jihar Kadunan ta roki jama'a da su kiyaye wajen ruwaito labarin tare da mutunta sirrin wadanda aka sacen. Ta kara da jawo hankalin jama'ar jihar da su bawa 'yan ta'adda kunya ta hanyar rungumar wadanda aka sace din. Ta kara da cewa, gudunsu ko kawo banbancin kabila ko addini ba abu ne nagari ba

Gwamnatin jihar Kaduna karakashin hgaorancin gwamna Malam Nasir ElRufai ya bukaci jama'ar jihar da su kiyaye tare da sa'ido akan harkar tsaro. ya kara da bukatar neman hadin kan jama'ar da jami'an tsaro don kawo karshen rashin tsaro da ya fara addabar jihar.

Wadanda aka sako din wadanda kananan yara sun fi yawa a cikinsu, zasu fuskanci rashin natsuwa tare da danginsu. Gwamnan ya bayyana cewa za a maida hankali wajen ganin natsuwarsu ta dawo kamar da.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel