Sarakuna sun roki shugaba Buhari ya bari Nnamdi Kanu ya shigo Najeriya don halartar jana'izar mahaifiyarsa

Sarakuna sun roki shugaba Buhari ya bari Nnamdi Kanu ya shigo Najeriya don halartar jana'izar mahaifiyarsa

- Wani sarki a kudancin Najeriya roki shugaban kasa Muhammadu Buhari alfarmar ya kyale Nnamdi Kanu ya shigo Najeriya

- Sarkin ya roki shugaban kasar ne bayan mutuwar mahaifiyar Nnamdi Kanu a makonnin da suka gabata, inda ya ce ya kamata a barshi ya shigo domin halartar jana'izar mahaifiyar ta shi

- Haka kuma Sarkin ya roki majalisar dinkin duniya da ta sanya baki akan wannan lamari domin a kyale Kanu ya shigo

Sarkin Orlu dake jihar Imo, Eze Gideon Ejike ya roki gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari da ta kyale shugaban masu gwagwarmayar kafa kasar Biafra, Nnamdi Kanu ya shigo Najeriya domin ya halarci jana'izar mahaifiyarsa da ta mutu a makonnin da suka gabata.

Sarkin ya bayyana hakan ne a wajen wani taro da ya halarta ranar Alhamis 24 ga watan Oktoban nan, "Kanu ba dan ta'adda bane, 'yan ta'adda kashe mutane suke yi, amma mu har yanzu bamu ga wani jini da Kanu ya zubar ba."

"Kanu ginshiki ne a wajen mu, saboda haka a kyale shi ya shigo Najeriya ya halarci jana'izar mahaifiyarshi kafin karshen wannan shekarar.

KU KARANTA: Karshen duniya: Yarinya 'yar shekara 9 ta rubutawa yaro dan shekara 9 wasikar soyayya

"Ya cancanci wannan damar a matsayin shi na danta na fari a kyale shi ya binne mahaifiyarsa."

Haka kuma Sarkin ya roki majalisar dinkin duniya da ta roki gwamnatin Najeriya domin ta kyale Kanu ya shigo Najeriya ayi bikin binne mahaifiyarshi ba tare da jami'an tsaro ko wasu sun kawo wata matsala ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel