Yanzu -Yanzu: An sako alkalin da aka yi garkuwa dashi

Yanzu -Yanzu: An sako alkalin da aka yi garkuwa dashi

- Masu garkuwa da mutane sun sako alkalin babbar kotun tarayya dake Akure

- An gano cewa, an sako alkalin ne da misalin karfe 2 na dare amma babu tabbacin an biya kudin fansa ko a'a

- Masu garkuwar da mutane sun bukaci naira miliyan 50 bayan da suka yi awon gaba da Abdul Dogo da direbansa

Masu garkuwa da mutane sun sako Abdul Dogo, Alkalin babbar kotun Akure da ke jihar Ondo.

'Yan bindiga sunyi garkuwa da Dogo ne a yankin Ibilo na Ede/Esua a yankin Akoko na jihar ondo inda yake komawa Akure daga Abuja.

Jaridar The Cable ta gano cewa an sako alkalin da wajen karfe 2 na dare amma ba ta tabbatar da an biya kudin fansa ko ba a biya ba.

KU KARANTA: Tsoffin tsagerun Niger Delta sun yi barazanar komawa ruwa, sun bada sharadi

An yi garkuwa da alkalin ne tare da direbansa inda suka bukaci kudin fansa har naira miliyan hamsin.

Wani ganau ba jiyau ba, ya ce, Dogo na cikin mota kirar SUV mai lamba HC 72FJ wacce mallakin babbar kotun tarayyar ce, lokacin da 'yan bindigar suka dinga harbi har suka dai yi awon gaba dashi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel