Kisan mutum 2 a Sokoto: Tambuwal ya kafa kwamitin bincike na mutum 10

Kisan mutum 2 a Sokoto: Tambuwal ya kafa kwamitin bincike na mutum 10

Gwamna Aminu Waziri Tambuwal na jihar Sokoto a ranar Juma’a 25 ga watan Oktoba, 2019 ya kafa kwamitin bincike na mutum 10, domin ya bi diddigin gaskiyar abinda ya faru tsakanin sojojin NAF da wasu mutum biyu da aka kashe a jihar.

Kwamishinan tsaro na jihar Sokoto, Kanal Garba Moyi ne ya wakilci gwamna a wurin taron kafa wannan kwamiti. Kuma ya bai wa kwamitin kwana 5 domin kawowa gwamnati rahoto.

KU KARANTA:Gwamnan APC ya kai ziyarar ba zata asibiti da makaranta a jiharsa

DCP Charles Mozie na hukumar CID shi ne zai jagoranci kwamitin, yayin da Abdulkadir Muhammad zai kasance sakataren kwamitin.

Sauran mambobin kwamitin sun fito ne daga hukumomin tsaron, sojin, DSS, NAF da jami’an tsaron farar hula na NSCDC.

Sarkin musulmi ma yana cikin kwamitin, inda Ubandoman Sabon-Birni, Alhaji Malami Malami Maccido da uban kasar Gagi, Alhaji Sani Umar Jabbi ke wakiltarsa.

Gwamna Tambuwal ya roki kwamitin da suyi kokari gudanar da bincike na gaskiya ba tare da nuna son kai ko kyashi ba.

Haka zalika ya bada tabbacin cewa, da rahoton binciken kwamitan gwamnati za ta dauki mataki na hukuncin da ya dace.

A wani labarin kuwa zaku ji cewa, Gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu ya kai ziyarar ba zata zuwa asibiti da wata makarantar firamare a jihar Legas.

A safiyar Alhamis 24 ga watan Oktoba ne gwamnan ya ziyarci wata asibiti dake Obalende ba tare da ma’aikatan asibitin sun san da zuwansa ba.

https://dailynigerian.com/sultan-9-others-to-investigate-soldiers-killing-of-civilians-in-sokoto/

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel