Gwamnan APC ya kai ziyarar ba zata asibiti da makaranta a jiharsa

Gwamnan APC ya kai ziyarar ba zata asibiti da makaranta a jiharsa

A ranar Alhamis 24 ga watan Oktoba, asibitin Onikan Health Centre dake Obalende a jihar Legas ta tarbi bakunci Gwamna Babajide Sanwo-Olu da misalin karfe 10 na safe.

Gwamnan ya kai ziyara asibiti ne ta ba zata domin ya duba kayan aiki da kuma yadda ma’aikatan ke gudanar da aikin na su a asibitin.

KU KARANTA:Zaben Gwamna: PDP ta mutu murus, da sannu za a mance da ita a jihar Kogi, inji Ohere

Dr Oreose Imosemi ne ya karbi Gwamna inda ya zagaya da shi wurare daban-daban inda ya ziyarci dakunan jinya. Babajide ya biya kudin maganin wasu daga cikin ‘yan jinyan da ba su da halin biyawa kansu.

Bayan ya kammala zagayen duba sassan asibitin, Babajide ya yi wata takaitacciyar tattaunawa da hukumar gudanarwar asibitin. Inda ya bayyana jin dadinsa bisa abinda ya gani, ya kuma yi kira a gare su da su yi kokari gyaran wadansu ‘yan kusakurai.

Daga asibitin, sai Gwamna Sanwo-Olu ya zarce zuwa makarantar firamaren St. Peters Anglican Nursery and Primary School dake Ikeja. Gwamnan ya dau tsawon lokaci a makarantar inda ya fadakar a kan muhimmancin tsaftar muhalli.

Da yake zantawa da daliban aji biyar na makarantar, Gwamnan ya ce da su kada su rinka bata muhallinsu saboda tsafta nada amfani kwarai da gaske.

Bugu da kari, Sanwo-Olu ya zagaya sauran azuzuwan makarantar domin duba kayayyakin karatu da yanayi azuzuwan. Ya bada tabbacin cewa matsalolin da ya gani za a dau mataki a kansu.

https://thenationonlineng.net/sanwo-olu-shocks-civil-servants-in-surprise-visit-to-lagos-school-hospital/

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel