An sauke nasarar wata Musulma 'yar tsere saboda ta sanya Hijabi

An sauke nasarar wata Musulma 'yar tsere saboda ta sanya Hijabi

- An soke nasarar wata matashiyar budurwar 'yar tsere a kasar Amurka saboda yanayin tufafin da ta sanya

- An soke nasarar budurwar ne mai suna Noor Alexandria Abukaram saboda ta sanya hijabi a lokacin da ake gasar tseren

- Noor ta bayyana cewa kowa ya san ita ce ta samu nasara a wannan gasar tseren, amma an soke nasarar ta saboda ta sanya hijabi

Wani lamari ya faru a yankin gabashin Ohio na kasar Amurka, wanda ke nuni da wariyar addini, domin kuwa an sauke nasarar wata budurwar 'yar tsere ne Musulma saboda yanayin shigar ta.

Budurwar mai suna Noor Alexandria Abukaram 'yar shekara 16 ta samu nasarar lashe gasar tseren da aka gabatar na tsawon kilomita biyar, wanda aka yi a yankin gabashin na birnin Ohio a ranar Asabar dinnan da ta gabata.

Sai dai kuma bayan samun nasarar Noor Abukaram, an sauke nasarar ta saboda nuna wariya ta addini da kuma yanayin irin shigar da tayi.

KU KARANTA: Bidiyo: Budurwa ta tumurmusa saurayinta a kasa bayan ta kama shi yana lalata da wata

Noor ta tabbatar da cewa an sauke nasarar ta ne bayan kowa ya tabbatar da cewa ita ce tayi nasara sakamakon sanya hijabi da tayi.

A cewarta masu gudanar da gasar ba su nuna mata cewa akwai illar sanya hijabi ba a lokacin da ake tantance yanayin tufafin da suka sanya.

Noor ta bayyana cewa tana amfani da hijabinta ne don haka addininta ya shardanta, kuma hijabi bai sabawa dokokin tsere ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel