Tsoffin tsagerun Niger Delta sun yi barazanar komawa ruwa, sun bada sharadi

Tsoffin tsagerun Niger Delta sun yi barazanar komawa ruwa, sun bada sharadi

- Tsoffin tsagerun yankin Niger Delta sun yi barazanar komawa ruwa matukar ba a waiwayesu ba nan da mako daya

- Sun bayyana cewa, sun kammala koyon sana'o'i karkashin shirin sasanci na fadar shugaban kasa amma an hanasu hakkokinsu don fara sana'a

- Sun roki shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya bada umarnin a fara biyansu hakkokinsu ko kuma su koma ruwa tsundum

Tsoffin tsagerun yankin Niger sunyi alkawarin komawa ruwa matukar ofishin sasancin ya ki basu dunkulinsu na farko tare da sauran hakkikinsu da yakamata nan da kwanaki 7.

Tsoffin 'yan tada kayar bayan sun bayyana cike da alhini cewa, duk da sun kammala koyon sana'o'in dogaro da kai karkashin shirin sulhu na fadar shugaban kasa, ofishin ya ki basu hakkokinsu don fara sana'o'i.

KU KARANTA: Akwai lauje cikin nadi: An tsinci gawa a Otal din wani tsohon gwamna

Sun yi kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya umarci shugaban shirin, farfesa Charles Dokubo da ya biya wadanda suka samu horarwar.

Shugaban masu wakiltar tsoffin tsagerun, Ati Jackson, bayan gama tattauna a garin Yenagoa, jihar Bayelsa, ya ce, sun bada jan kunne na karshe kenan.

Jackson ya ce, kungiyar tayi zanga-zangar lumana a makon da ya gabata amma ya ce laifin duk yana kan Dokubo ne.

Ya ce: "Cibiyar horarwa ta Ezonebi ta kammala horarwar watanni 6 akan sana'o'i ga mutane masu yawa karkashin shirin sasancin amma har yanzu shiru kake ji an hanasu hakkokinsu."

"Wakilan sunyi zanga-zangar luman a makon da ya gabata. Suna bukatar hakkokinsu ne ko kuma su koma ruwa."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel