Majalisar tarayya ta dau zafi, ta juyawa Minista Sadiya Umar Farouq baya

Majalisar tarayya ta dau zafi, ta juyawa Minista Sadiya Umar Farouq baya

- Kwamitin majalisar dattawa na fatattakar talauci ya juyawa ministar walwala da jin kan 'yan kasa, Sadiya Faruk, baya

- Shugaban kwamitin ya fusata ne sakamakon rashin kawo kwafin kasafin kudin 2019 yayin kare na 2020

- An dage cigaba da zaman har zuwa ranar Litinin mai zuwa da misalin karfe 10 na safe

Kwamitin majalisar dattawa na fatattakar talauci ya juyawa ministar walwala da jin kan 'yan kasa, Hajiya Sadiya Umar Farouq baya. Kwamitin dai yaki amincewa ministar ne da ta kare kasafin tattalin arzikin ma'aikatar na shekarar 2020.

Shugaban kwamitin, Sanata Lawan Yahaya Gumau, ya ce, sun dau matakin ne saboda ma'aikatar bata bawa kwamitin kasafin kudinsu na shekarar 2019 ba.

KU KARANTA: Yadda na samu digiri har biyu a gidan gyaran hali - Tsohon dan fursuna

Gumau, wanda yayi magana a hasale, yace kwamitin ba zai lamunci dabi'ar rashin da'ar da masu bada shawara na musamman ga shugaban kasa suka nuna ba yayin rakiya ga ministar don kare kasafin kudin.

"Mai girma minista, mun san cewa ke sabuwa ce a nan. Amma wadanda suka rakoki sun sani sarai cewa sai an bada kwafin kasafin kudi na shekarar 2019 kafin a kare na 2020. Ba mu takurasu sai sun kawosu ba yayin kare na 2019. A tunanina mun gwada juriya kuma saboda mutanen da muke shugabanta ne," in ji shi.

Ya dage cigaba da zamn zuwa karfe 10 na safen ranar Litinin tare da jan kunnen cewa a bayyan duk takardun da ake bukata kafin ranar.

"Ina mai bada hakuri ga mai girma minista saboda ita sabuwa ce a nan, amma ga masu bada shawara ta musamman su biyu, bana ban hakuri," ya kara.

A maida martaninta, ministar ta bada hakuri ga kwamitin. Ta kara da bayyana musu cewa, a rubutaccen kasafin kudin da ka kawo, an hado da na'urar zamani mai dauke da kasafin kudin shekarar 2019.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel