An gurfanar da dan majalisa kan amfani da sakamakon WAEC ta bogi

An gurfanar da dan majalisa kan amfani da sakamakon WAEC ta bogi

A ranar Juma'a ne aka gurfanar da dan majalisar jihar Edo, Ugiagbe Dumez a wata babban kotun jihar da ke zamanta a Benin kan zargin mallakar takardan bogi da yin sojan gona. Mista Dumez mai shekaru 45 da wani mutum da har yanzu ake nema ne aka ce sun aikata lafin a shekarar 2001.

Daily Nigerina ta ruwaito cewa an gurfanar da wanda ake zargin ne gaban Mai Shari'a Ohimai Ovbiagele.

Sai dai dan majalisar bai hallarci kotun ba don ya amsa tambayoyi kan tuhumar da ake masa.

A cewar karar da aka karanto a kotun, a shekarar 2001, Mista Dumez da wani da ake nema sun hada baki sun aikata laifin buga takardan bogi.

DUBA WANNAN: Na yi wa 'ya'ya na biyu fyade ne don gwada kuzari na - Mahaifi

An ce dan majalisar ya hada takardan sakamakon jarrabawar kammala sakandare ta WAEC mai lamba NGWASSCP 1230734 a Disamban 2001 da sunan Ugiagbe Onaiwu Dumez mai lambar jarabbawa ta 5131293070 ta hanyar canja hoton da ke kan takardan kuma ya maye gurbinsa da nasa.

An ce wanda ake zargin ya hada baki da wanda ya gudun don aikata wannan laifin.

Ya kuma yi karyar cewa shine ya rubuta jarrabawar a maimakon wanda ainihin hotonsa ke kan takardan.

An ce dan majalisar ya canja sunar wanda ya rubuta jarbbawar da gangan wanda hakan ya sabawa doka.

Bayan karanto karar, gwamnatin jihar ta Edo ta ce za ta amshe shari'ar da kwamishinan jihar Edo a matsayin mai shigar da kara.

Lauyan jihar, Mista Peter Ojo ya ce karbe shari'ar da jiha ta yi ya yi dai-dai da sashi na 212 na kudin tsarin mulkin Najeriya.

Ya ce 'yan sanda sun bayar da belin Mista Dumez bayan an kama shi a Abuja kuma ya bayar da tabbacin zai kawo shi kotu a ranar da za a cigaba da sauraron shari'ar.

Mista Obviagele ya dage cigaba da sauraron shari'ar zuwa ranar 1 ga watan Nuwamba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel