Hukumar kwastam ta cika hannu da buhu 149 na haramtacciyar shinkafa a Kaduna

Hukumar kwastam ta cika hannu da buhu 149 na haramtacciyar shinkafa a Kaduna

Jami’an hukumar yaki da fasa kauri na Najeriya, watau Kwastam, reshen jahar Kaduna sun kama wasu tarin buhunan shinkafa yar kasar waje da aka shigo dasu Najeriya ta haramtacciyar hanya data kai buhu 149.

Rahoton kamfanin dillancin labarun Najeriya, NAN, ta bayyana cewa kaakakin hukumar, Abubakar Usman ne ya bayyana haka cikin wata sanarwa daya fitar a garin Kaduna a ranar Juma’a, 25 ga watan Oktoba.

KU KARANTA: Malaman jahar Kaduna zasu gudanar da zanga zangan rashin albashin watanni 5

Usman yace sun kama shinkafar wanda darajarta yah aura naira miliyan 3.5 a garejin mota dake Mando a daidai lokacin da ake kwancesu daga cikin buhunansu ana sake zubasu a cikin sabon buhunan shinkafar kamfanunuwan gida ta yadda zasu yi basaja tamkar shinkafar gida ce a cikin buhunan.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Usman yana cewa manufar wadanda suka shigo da shinkafar shine su zarce da ita zuwa jahar Legas, amma basu samu nasara ba bayan jami’an kwastam sun samu bayanan sirri, suka yi ma wurin dirar mikiya, sai dai yace basu kama kowa ba.

“Zamu cigaba da aikinmu don tabbatar mun kawar da duk wasu masu fasa kauri da masu daure musu gindi, za kuma mu cigaba da kwace kayan fasa kauri, tare da tabbatar da duk masu fasa kauri sun yi ta tafka asara har sai sun saki wannan mummunan sana’a tasu.” Inji shi.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel