Gidan Malam Owotutu: Gardawa 5 suka yi min fyade, na zubar da ciki har sau 3 - Budurwa

Gidan Malam Owotutu: Gardawa 5 suka yi min fyade, na zubar da ciki har sau 3 - Budurwa

Wata budurwa mai shekaru 20, Laide Arikewuyo, daya daga cikin wadanda aka ceto daga gidan kangarraru mara rajista a Ilori na jihar Kwara ta bayyana yadda 'yan uwan mai gidan, Mallam AbdulRaheem Owotutu ke zina da ita ba kakautawa.

Rundunar 'yan sandan jihar a ranar Alhamis ne suka nuna wa manema labarai mata, mata da yara kanana da suka ceto a gidan da ke yankin Gaa'Odota.

Ya yayin da ta ke bayar da labarin azabar da ta sha a gidan, Miss Arikewuyo ta zargi wadanda aka bawa aikin kulawa da su da laifin cin zarafinsu.

Ta ce iyayenta ne suka kai ta gidan Mallam Owotutu.

DUBA WANNAN: Na yi wa 'ya'ya na biyu fyade ne don gwada kuzari na - Mahaifi

Ta ce: "Iyaye na ne suka kai ni gidan Mallam Owotutu da suka gano inda na tsere na buya.

"Na tsere daga gida ne don iyaye na basa kulawa da ni amma da suka gano inda na koma da zama sai suka kai ni gidan Mallam kimanin shekaru 5 da suka shude.

"Wasu daga cikin 'ya'yan Mallam da 'yan uwansu sun sha yin zina da ni barkatai. A kalla mutane 5 da ke kula da mu a gidan kuma zan iya tunawa na samu juna biyu kimanin sau uku amma su kan bani wani magani da zan sha don cikin ya zube."

Wani da aka ceto a gidan, Tope Collins Owonifaari ya ce wasu mutane da bai sansu ba ne suka dako shi daga Legas kawai sai ya tsinci kansa a gidan mara tsafta inda aka cinkusa su a wuri daya.

Ya ce: "Wasu mutane da ban san su bane suka kamo ni ne daga motar haya a Legas misalin karfe 4 na asubahi na ranar 20 ga watan Oktoban 2019, ba zan iya fadin yadda aka yi na tsinci kai na a gidan nan ba inda ake cakwuda mu wuri guda ba tare da mun fita waje ba."

Ya kara da cewa ya kashe kwanaki hudu a gidan kafin 'Yan sanda su ceto su.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel