Yanzu Yanzu: Gwamna Yahaya Bello ya sake samun karfi yayinda kotu ta yi watsi da karar da ke neman hana shi takara
- Babbar kotun tarayya ta yi watsi da bukatar sauraron karar dake neman a hana Gwamna Yahaya Bello takara a zaben wanda aka shirya gudanarwa a ranar 16 ga watan Nuwamba a jihar Kogi
- Yar takara a inuwar jam’iyyar Social Democratic Party (SDP), Natasha Akpoti ce ta shigar da karar
- Ta zargi Bello da yin rijista sau biyu a matsayinsa na mai zabe a 2011 da 2017 don haka ta nemi a hana shi takara
Kasa da wata guda kafin zaben gwamnan jihar Kogi, wata babbar kotun tarayya ta yi watsi da bukatar sauraron karar dake neman a hana Gwamna Yahaya Bello takara a zaben wanda aka shirya gudanarwa a ranar 16 ga watan Nuwamba a jihar Kogi.
Justis Ijeoma OJukwu, a hukuncin da ta yanke a ranar Juma’a, ta tura karar da wata yar takara a inuwar jam’iyyar Social Democratic Party (SDP), Natasha Akpoti, zuwa kotun reshen Lokoja.
Akpoti, a karar da ta shigar mai lamba FHC/ABJ/CS/122/2019 ta yi ikirarin cewa Bello ya yi rijista sau biyu a matsayinsa na mai zabe a 2011 da 2017, don haka tana rokon kotu da ta hana shi yin takarar kowani mukami har zuwa nan da shekara 10.
KU KARANTA KUMA: Salamatu ta ce rayuwarta na fuskantar barazana don ta fallasa A.B Umar na KASU
A halin da ake ciki, Legit.ng ta rahoto a baya cewa Kwamishinan kananan hukumomi na jihar Kogi, Engr Abubakar Ohere ya ce PDP ta mutu murus a jihar Kogi kuma saura kadan ta zama tarihi a jihar.
Abubakar ya fadi wannan maganar ne ranar Alhamis 24 ga watan Oktoba a lokacin da yake jagorantar kamfen din gwamna a shiyyar Kogi ta tsakiya.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng