Zaben Gwamna: PDP ta mutu murus, da sannu za a mance da ita a jihar Kogi, inji Ohere

Zaben Gwamna: PDP ta mutu murus, da sannu za a mance da ita a jihar Kogi, inji Ohere

Kwamishinan kananan hukumomi na jihar Kogi, Engr Abubakar Ohere ya ce PDP ta mutu murus a jihar Kogi kuma saura kadan ta zama tarihi a jihar.

Abubakar ya fadi wannan maganar ne ranar Alhamis 24 ga watan Oktoba a lokacin da yake jagorantar kamfen din gwamna a shiyyar Kogi ta tsakiya.

KU KARANTA:Kuyi hakuri da tsadar kaya sakamakon rufe kan iyaka – Osinbajo

Kamar yadda ya ce, aikin da Gwamna Yahaya Bello yayi a cikin shekaru uku da rabi da suka shude ya tabbatarwa jam’a irin kyakkyawar niyyar APC.

Ya kuma kara da cewa, zaben gwamnan jihar dake tafe a ranar 16 ga watan Nuwamba, 2019 wata dama ce da mutanen yankin nasa za su nunawa duniya cewa, bayan APC babu wata jam’iyyar siyasan da suka sani.

Bugu da kari, ya yi kira ga magoya bayan jam’iyyar tasu da su guji tayar da hankali a lokacin zaben, inda ya ce su gudanar da harkokinsu cikin kwanciyar hankali da lumana.

A wani labarin kuwa za ku ji cewa, wata kungiya da ke bibiyar lamuran zabe wadda ake yiwa take da CTA, ta bayyana damuwarta game da aukuwar rikice-rikice daban-daban a Kogi da Bayelsa.

A don haka kungiyar ta yi kira ga jami’an tsaro da su tashi tsaye domin tabbatar da tsaron mutane a lokacin da ake kada kuri’a da kuma bayan an kammala zaben gaba daya.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel