Salamatu ta ce rayuwarta na fuskantar barazana don ta fallasa A.B Umar na KASU

Salamatu ta ce rayuwarta na fuskantar barazana don ta fallasa A.B Umar na KASU

Wata tsohuwar dalibar jami’ar Ahmadu Bello dake Zaria, Salamatu Bello, wacce ta yi ikirarin cewa wani tsohon lakcara na jami’ar mai suna A.B Umar ya yi lalata da ita, ta bayyana cewa rayuwarta na cikin hatsari akan zanga-zangar akan daukar malamin aiki da jami’ar jihar Kaduna (KASU) ta yi.

Salamatu ta karyata zargin cewa ramuwar gayya take yi akan lakcaran.

Salamatu, wacce ta mallaki digiri na biyu tace lamarin ya afku ne a tsakaninta da Mista Umar a lokacin da take dalibar difloma a ABU a 2010.

Ta yi hira da jaridar Daily Trust a lokacin zanga-zangarta a hanyar Bida dake birnin jihar.

Ta yi zargin cewa rayuwarta na cikin hatsari yayinda wasu da bata sani ba suke mata barazana.

KU KARANTA KUMA: Kotun Kano ta tsare wasu maza 2 da mace 1 kan laifin kwartanci

Da farko dai mun ji cewa Jami'ar Jihar Kaduna (KASU), a ranar Laraba ta dauki mataki kan daya daga cikin malamanta, Mista Bala Umar da aka fi sani da A.B. Umar kan zargin da ake masa na neman yin lalata da daliba don ya bata maki.

A taron da muhukuntar Jami'ar suka yi a ranar Laraba, KASU ta ce an kafa kwamiti don bincike kan zargin da ake yi wa Umar bayan zanga-zangar da wata mata tayi.

Matar da ba a fadi sunan ta ba, ta yi ikirarin cewa cewa Umar bai cancanta ya zama malami a jami'ar ba domin an kore shi ne daga Jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria kan yin lalata da daliba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel