Jihar Adamawa ta dage ranar zabe, ta sanar da ranar da za'ayi

Jihar Adamawa ta dage ranar zabe, ta sanar da ranar da za'ayi

- Hukumar zabe mai zaman kanta ta jihar Adamawa, ta dage ranar zaben shuwagabannin kananan hukumomi

- An dage ne sakamakon 'yan matsalolin da hukumar zaben mai zaman kanta ta jihar ke fuskanta

- Tun a watan Yuli ne aka mika akalar mulkin kananan hukumomin zuwa wajen kwamitin rikon kwarya

Hukumar zabe mai zaman kanta ta jihar Adamawa, ta sanar da sabuwar ranar zaben da za a yi a jihar. Hukumar ta bayyana cewa, an yi sabon jadawalin zaben.

ADSIEC ta ce, an dage zaben ne sakamakon wasu matsalolin da hukumar ke fuskanta.

A takardar da shugaban hukumar, Isa Shetima, yasa hannu, ta nuna cewa, za a kammala karbar cikakken fom din ‘yan takarar ne daga ranar 20 zuwa 25 ga watan Oktoba.

KU KARANTA: Yanzu - Yanzu: An kara bankado wani gidan kangararru a jihar Kwara

Jadawalin ya nuna cewa, za a fidda sunan ‘yan takarar da suka tsallake matakin tantancewa daga hukumar daga ranar 11 zuwa 13 ga watan Nuwamba. Ranar karshe kuma ta yakin neman zabe zata zama 6 ga watan Disamba.

A halin yanzu, duk kananan hukumomi 21 na jihar Adamawa na hannun ‘yan rikon kwarya ne.

An zabi kwamitin rikon kwaryar ne a watan Yuli bayan da majalisar jihar ta aminta da hakan daga Gwamna Ahmadu Fintiri.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel