Kuyi hakuri da tsadar kaya sakamakon rufe kan iyaka – Osinbajo

Kuyi hakuri da tsadar kaya sakamakon rufe kan iyaka – Osinbajo

Mataimakin shugaban kasan Najeriya, Yemi Osinbajo ya roki ‘yan Najeriya cewa su yi hakuri su jure tsadar kayayyaki a sakamakon rufe kan iyakar kasar.

Osinbajo ya ce an rufe kan iyakar saboda manoman Najeriya sun bunkasa a fannin noman da suke yi. Ya fadi wannan maganar ne a Benin City babban birnin jihar Edo.

KU KARANTA:Ganduje ya raba kayan makaranta da littafan karatu kyauta ga daliban firamare a Kano

Da yake jawabi a wurin taron al’adun gargajiya a Benin City, Mataimakin shugaban kasa ya ce, daya daga cikin dalilan rufe kan iyakar shi ne domin a sanya kasashen dake makwabtaka da Najeriya su dau matakan da suka dace a kan iyakokin.

Ya kuma ce, sauran kasashen da suka cigaba a duniya ba su bari ana shigo masu da abinci sai dai su noma da kansu.

Ga kadan daga kalaman Osinbajo a wurin taron: “Daga cikin dalilan da suka tilasta mana rufe kan iyaka akwai fasa kwauri da aka jima anayi. Idan muka cigaba da barin China na shigowa da kaya kasarmu zamu kashe noman da muke yi.

“A sakamakon hakan kuwa mutane da yawa za su rasa aikin yi. Kan a ji dadi dole sai an sha wuya, dukkanin kasashen duniyar nan da suka cigaba sai da suka haramta shigowa da kaya cikin kasaru.

“Ina kira ga mutanenmu da su kara hakuri, saboda bayan wuya sai dadi. A yanzu hakan na san akwai tsadar kaya a kasuwa, kuma wannan na faruwa ne saboda an hana fasa kwauri. Yin hakan kuwa shi ne zai ba wa manomanmu damar noma abinda zamu ciyar da kanmu da shi.” Inji Osinbajo.

https://thenationonlineng.net/endure-pains-of-border-closure-osibanjo/

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel