Yadda na samu digiri har biyu a gidan gyaran hali - Tsohon dan fursuna

Yadda na samu digiri har biyu a gidan gyaran hali - Tsohon dan fursuna

- Wani wanda ya fito daga gidan gyaran hali na jihar Enugu ya bayyana yadda ya samu digiri har biyu yayin da yake zaman gidan

- Duk da karatu a cikin irin yanayin ba mai sauki bane, ya sanar da cewa, jajircewa da hakuri sun taka rawar gani

- Ganin cewa ba aikin da zai samu da takardar kammala sakandire, hakan yasa ya kwantar da hankalinsa wajen neman madafa

Wani tsohon dan gidan gyaran hali na Najeriya da ya zauna a gidan na jihar Enugu, Adeniyi Theophilus, ya samu digiri har biyu yayin da yake gidan gyaran hali.

Adeniyi ya sanar da kamfanin dillancin labarai a jihar Enugu a ranar Juma’a cewa, ya yi amfani da damrsa wajen yin karatu har na digiri biyu daga NOUN lokacin yana tsare.

“Mun yi mamaki domin kuma bamu yarda akwai jami’a a cikin gidan gyaran halin ba,” in ji shi.

KU KARANTA: Yanzu - Yanzu: An kara bankado wani gidan kangararru a jihar Kwara

“Shugaban gidan fursunan, Mustapha Attah ne ya dinga bamu kwarin guiwa tunda muna da takardun kammala makarantar sakandire. Kuma gidan gyaran halin ne suka biya mana rabin kudin makarantar namu. Duk da ba abin wasa bane samo sauran rabin kudin tare da kudin siyan takardu.”

Adeniya dan karamar hukumar Nkanu ta gabas ne a jihar Enugu. An tsaresa a gidan gyaran halin ne yana jiran hukunci a 2010.

Yace, rashin natsuwar da ke tattare da zaman gidan fursuna kadai ya isa ya hana mutum karatu. Amma da juriya tare da jajircewa, duk sun wuce.

“Wani abinda ya kara min kwarin guiwa shine, idan na bar gidan yarin, bazan samu aikin yi mai kyau da kwalin kammala karatun sakandire ba.”

Ya ce, a shekarar 2015, a cikin ‘yan gidan 25 da suka fara karatun, shi kadai ne ya iya kammalawa

“Jami’ar ta bani kyautar naira dubu hamsin wacce nayi amfani da ita wajen zarcewa digirina na biyu a shekarar.”

A halin yanzu dalibi ne a jami’ar Najeriya dake Nsukka bayan barin gidan gyaran halin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel