Soyayya ruwan zuma: Ya auri abar kaunarsa yana da shekaru 96 ita tana da shekaru 73

Soyayya ruwan zuma: Ya auri abar kaunarsa yana da shekaru 96 ita tana da shekaru 73

- Kauyen manoma mai suna Kiyi da ke Abuja ya cika da murna da dauki a ranar Alhamis da ta gabata

- Tsoho mai shekaru 96 a duniya ya auri mata masoyiyarsa mai shekaru 73 a duniya

- Hakan kuwa ya jawo cece-kuce a kauyen don wasu na zargin rashin kula ce tasa ya yi auren bayan rasuwar matarsa ta farko

Kauyen manoma mai suna Kiyi da ke Abuja ya cika da dauki a ranar Alhamis, 17 ga watan Oktoba. Pa AbdRahman Munse-Bwaye mai shekaru 96 ya cika burinsa inda ya auri masoyiyarsa, Rukaya Yamwa-Piri, mai shekaru 73 a duniya.

Kamfanin dillancin labarai ya ruwaito cewa, an daura auren a kauyen Piri ne da ke karamar hukumar Kwali.

Amaryar da ta tare a gidan mijinta bayan an daura auren ta sanar da kamfanin dillancin labarai cewa, “ina farincikin auren mutum nagari kamar AbdRahman”.

KU KARANTA: Yanzu - Yanzu: An kara bankado wani gidan kangararru a jihar Kwara

Rukaya ta sanar da kamfanin dillancin labarai cewa, an daura aurensu da rabin ranta ne a kauyen Piri dake karamar hukumar Kwali ta jihar Abuja.

Pa Munse na daya daga cikin tsofaffin kauyen Kiyi dake karamar hukumar Kuje . Kamfanin dillancin labarai ya ruwaito cewa, mutane da yawa sun shawarcesa da kada yayi auren ganin cewa ya tsufa.

Wasu mutanen sun zargi cewa sirikansa basa kula dashi, amma ya sanar dasu cewa ko kusa ba hakan bane. Ya sanar dasu cewa, matarsa zata fi kula dashi.

Matar Pa Munse ta farko, Hajiya Zainab Godobe, ta rasu ne a shekarar 2008.

“Na auri wata mata da mijinta ya rasu bayan rasuwar matata ta farko, amma ‘ya’yanta sunzo sun tafi da ita bayan shekaru inda suka barni ina gwauranci. Na nemi auren Rukaya kuma Ubangiji ya nufa. Ina matukar farinciki.”

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel