Malaman jahar Kaduna zasu gudanar da zanga zangan rashin albashin watanni 5

Malaman jahar Kaduna zasu gudanar da zanga zangan rashin albashin watanni 5

Kungiyar Malaman jahar Kaduna, NUT, reshen jahar Kaduna tana tausan ma’aikatan jahar Kaduna da suka kwashe tsawon watanni 5 ba tare da samun albashi ba da su yi hakuri kada su gudanar da zanga zangar da suke shiryawa.

Kamfanin dillancin labarun Najeriya, NAN, ta bayyana cewa NUT na kira ga sabbin malaman da aka dauka da suke fuskantar wannan matsala da kada su yi garaje, su kara hakuri a kan wannan matsala da cewa za’a warwareta.

KU KARANTA: An goga gemu da gamu tsakanin Malami, Sanata Ahmad Lawan da Gbajabiamila

Shugaban kungiyar, Ibrahim Surajo ya bayyana haka cikin wata sanarwa daya fitar a ranar Juma’a inda ya nemi Malaman su kara hakuri har zuwa lokacin da gwamnati da kungiyar zasu kammala tattaunawa a kan matsalar.

“Ya kamata a sani cewa akwai wasu Malaman makarantun firamari a wasu kananan hukumomi wanda a yanzu haka sun fara samun albashinsu, kuma sabon karancin albashi, kuma muna tabbatar ma malamai cewa gwamnati ta amince a biyasu albashinsu na Oktoba.

“Haka zalika kungiyar NUT ta nesanta kanta daga zanga zangar da wasu malamai suke nufin shiryawa akan batun tsaikon da aka samu wajen biyan albashin watan Satumba, kungiyarmu bata tare da wannan kungiya, kuma ba zamu taba shiga cikin zanga zangar ba, don haka masu shirin yin zanga zangar su bari.”

A hannu guda kuma Sijaro ya musanta batun da ake yayatawa na cewa wai NUT ta kara kudin da malamai suke tarawana Endwell zuwa N4000 a kowanne wata, inda yace ba gaskiya bane.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel