An jefa wani matashi kurkukun Kirikiri saboda jifan Yansanda da duwatsu

An jefa wani matashi kurkukun Kirikiri saboda jifan Yansanda da duwatsu

Wani matashi dan shekara 30 dake farautar aikin yi, Sulaiman Agboola ya jefa kansa cikin tsaka mai wuya bayan kotu ta bada umarnin a garkame shi a kurkukun Kirikiri sakamakon kamashi da ta yi da laifin cin zarafin Yansanda.

Rahoton kamfanin dillancin labarun Najeriya, NAN, ta bayyana cewa Sulaiman ya amsa laifinsa yayin da aka gurfanar dashi gaban kotun majistri dake karkashin jagorancin mai sharia M.O Tanimola, da wannan ne Alkain ya bukaci a sakaya shi a kirikiri dake Apapan jahar Legas.

KU KARANTA: Shafaffu da mai: Diyar Goje ta samu kulawa ta musamman domin darewa mukamin kwamishina

Majiyar Legit.ng ta ruwaito dansanda mai kara, Sufeta Aondohemba Koti ya bayyana ma kotu cewa wanda ake kara yana tara matasa a titin Agege cikin unguwar Oshodi yana sayar musu da tabar wiwi.

“A haka ne a ranar 17 ga watan Oktoba da misalin karfe 9.45 na dare suka fara jifan motar Yansanda da duwatsu da kwalabe dake aikin sintiri, haka nan koda Yansanda suka yi kokarin kamashi, sai ya kokarin tserewa, ya cigaba da jifan Yansanda duwatsu da kwalabe, amma daga bisani muka kamashi, abokansa kuma suka tsere.” Inji Dansandan.

Wannan laifi da ake tuhumar Sulaiman da aikatawa ya saba ma sashi na 42, 44, 56, 168, 174 da 411 na kundin hukunta manyan laifuka na jahar Legas na shekarar 2014.

Daga karshe Alkalin kotun ya dage cigaba da sauraron karar zuwa ranar 31 ga watan Oktoba domin samun cikakken bayani daga masu kara da kuma yanke hukunci.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel