Yanzu Yanzu: Kotu ta tsare Maina a gidan kurkuku

Yanzu Yanzu: Kotu ta tsare Maina a gidan kurkuku

Wata babbar kotun tarayya da ke Abuja, ta yi umurnin tsare tsohon Shugaban hukumar fansho dake fuskantar shari’a, Abdulrasheed Maina, a gidan kurkuku.

Justis Okon Abang ya bayar da umurnin tsare shi biyo bayan wata bukata da hukumar yaki da cin hanci da rashawa (EFCC) ta nema bayan ya ki amsa tuhume-tuhume 12 ake yi masa.

Alkalin ya kuma dage shari’an har zuwa ranar 30 ga watan Oktoba domin shari’an da kuma 19 ga watan Nuwamba domin sauraron bukatarsa na neman beli kafin gurfanar dashi.

A baya Legit.ng ta rahoto cewa tsohon shugaban kwamitin inganta kudin fansho, AbdulRashid Maina, ya dira babbar kotun tarayya dake Abuja yayinda hukumar hana almundahana da yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa wato EFCC ke gurfanar da shi.

Maina ya isa kotun ne tare da 'dansa, Farouq, wanda aka damkesu tare bayan yayi kokarin harbin jami'an DSS da bindiga.

Hukumar na zarginsa da laifin almundahanar kudaden yan fanshi N100 billion.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Kotu ta yi watsi da yan takarar gwamna 2 gabannin zaben Kogi

Babban kotun tarayya dake Abuja ta bada umurnin sadaukarwa gwamnatin tarayya dukiyoyi 23 da ake kyautata zaton na tsohon shugaban gyara harkan fansho, Abdulrashid Maina.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel