Yanzu Yanzu: Kotu ta yi watsi da yan takarar gwamna 2 gabannin zaben Kogi

Yanzu Yanzu: Kotu ta yi watsi da yan takarar gwamna 2 gabannin zaben Kogi

Wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta tabbatar da matsayar hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) na watsi da wasu yan takarar gwamna guda biyu a zaben Kogi mai zuwa.

Kotun, a cewar jaridar The Nation, ta riki hukuncin hukumar INEC na watsi da yan takarar jam’iyyun Allied Congress Party of Nigeria (ACPN) da Freedom and Justice Party (FJP).

Alkalin da ke jagorantar shari’an, Justis Ijeoma Ojukwu, ya yanke hukunci biyu a ranar Juma’a, 25 ga watan Oktoba, inda ya tabbatar da hukuncin INEC na watsi da yan takarar.

Hukuncin kotun ya kasance bisa ga hujjar cewa doka ta haramta masu yin haka.

A cewar Justis Ojukwu, INEC ta yanke hukuncinta ne bisa ga karfin kundin tsarinta na watsi da yan takarar bayan gano cewa jam’iyyun biyu sun ki bin ka’idar wa’adinta don gabatar da jein yan takararsu da kuma fam dinsu.

KU KARANTA KUMA: Zuwan Buhari Rasha zai gyara barnar da PDP ta yi na tsawon shekaru 16 - Princewill

A wani labarin kuma mun ji cewa Mambobin majalisar wakilai a karkashin inuwar jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) sun bayyana tsige mataimakin gwamnan jihar Kogi, Simon Achuba a matsayin ba bisa ka’ida ba.

Kamfanin dillancin labaran Najeriya ta ruwaito cewa yan majalisar sun bayyana matsayarsu ne a wani jawabi dauke da sa hannun shugabansu, Kingsley Chinda daga jihar Rivers.

Mambobin majalisar wakilan sun bukaci majalisar dokokin kasar, kungiyoyin jama’a da yan Najeriya masu fada a ji da su dauki mataki domin kare damokradiyya daga durkushewa kwata-kwata.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel