Albashi: Fusatattun ma'aikata sun rufe shugaban karamar hukuma a ofishinsa

Albashi: Fusatattun ma'aikata sun rufe shugaban karamar hukuma a ofishinsa

Fusatattun ma'aikata a karamar hukumar Doma na jihar Nasarawa sun rufe shugaban karamar hukuma, Rabo Sani na tsawon lokaci fiye da awanni uku kan rashin biyansu albashinsu na watan Satumba.

Mai'aikatan suna zargin shugaban karamar hukumar ta jefa su cikin walwalhu saboda rashin zuwa ofishinsa da ba ya yi.

Binciken da Northern City News ta yi a ranar Alhamis 24 ga watan Oktoba ya nuna cewa yunkurin da sojoji na Barikin 123 da ke Doma suka yi yunkurin yi bai yiwu ba don ma'aikatan sun ki sauraransu.

DUBA WANNAN: Bin diddigi: Shin gaskiya ne CIA ta yi hasashen cewa Najeriya za ta rushe kamar yadda Jega ya fadi?

Bayan da hankulan ma'aikan ya kwanta, shugaban karamar hukumar ya yi musu bayanin cewa an samu matsala ne saboda bashin naira miliyan 100 da tsohon shugaban karamar hukumar ya bar masa. Ya kuma ce wata matsalar da ake fuskanta shi ne ma'aikatan karamar hukumar sun yi yawa.

Sani ya ce, "Mun fara fuskantar matsaloli ne tun bayan da aka bawa kananan hukumomi 'yancin kansu don a baya muna amfani da kudaden kananan hukumomin da ba su da nauyi da yawa mu biya albashi.

"Daga watan Yuni, Yuli da Augusta, sai da muka yi ciko da harajin kayan masarufi na VAT kafin muka iya biyan albashi amma yanzu kwamitin kananan hukumomi ta hana mu yin hakan don kudin VAT na ayyukan more rayuwar al'umma ne ba albashi ba."

Ya kuma bayyana cewa karamar hukumar ta yi amfani da fiye na naira miliyan 30 don kafa wutan tituna na tsawo kilomita 1 daga fadar Andoma kuma ana fara aikin wani titin na mita 300. Ya ce a watan Augusta, karamar hukumar ta samu tsaiko na naira miliyan 9.2 wadda hakan ya shafi biyan albashi na watan Satumba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel