KASU ta dakatar da malami kan 'lalata da dalibai'

KASU ta dakatar da malami kan 'lalata da dalibai'

Jami'ar Jihar Kaduna (KASU), a ranar Laraba ta dauki mataki kan daya daga cikin malamanta, Mista Bala Umar da aka fi sani da A.B. Umar kan zargin da ake masa na neman yin lalata da daliba don ya bata maki.

A taron da muhukuntar Jami'ar suka yi a ranar Laraba, KASU ta ce an kafa kwamiti don bincike kan zargin da ake yi wa Umar bayan zanga-zangar da wata mata tayi.

Matar da ba a fadi sunan ta ba, ta yi ikirarin cewa cewa Umar bai cancanta ya zama malami a jami'ar ba domin an kore shi ne daga Jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria kan yin lalata da daliba.

DUBA WANNAN: Bin diddigi: Shin gaskiya ne CIA ta yi hasashen cewa Najeriya za ta rushe kamar yadda Jega ya fadi?

Mataimakin shugaban Jami'ar, Fafesa Abdullahi Ashafa wanda ya jagoranci taron ya ce KASU ba za ta amince da wani halin rashin da'a ba daga ma'aikatan ta kuma za ta dauki mataki kan duk wanda aka samu da laifi.

Ashafa ya ce Jami'ar tana cigaba da bincike a kan zargin da ake yi wa Umar.

Ashafa ya ce an kafa kwamitoci biyu; daya don bincike kan zargin da ak yi wa Umar, sannan na biyun kuma zai yi bincike kan afkuwar wasu abubuwa da ya shafi malamai da sauran ma'aikata wadanda ba su koyarwa.

DVC din ya ce duk da cewa Umar ba koyarwa ya ke yi ba, an dakatar da shi nan take don a gudanar da bincike.

Ya ce, "Idan an same shi da laifin lalata wa jami'ar suna, za a dakatar da shi, a zabtare rabin albashinsa kuma a kai kararsa gaban majalisar jami'a don daukan mataki na karshe."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel