Rashin tsaro: IG zai shiryawa jami’an ‘yan sanda taro na musamman na kwana 3

Rashin tsaro: IG zai shiryawa jami’an ‘yan sanda taro na musamman na kwana 3

-Rundunar 'yan sandan Najeriya za ta gudanar da wani taro na kwana uku a Legas

-Taron zai soma ne daga ranar Litinin 28 zuwa Laraba 30 ga watan Oktoba

-Shugaba Muhammadu Buhari shi ne wanda zai jagoranci bude taron, kamar yadda DCP Frank Mba ya shaida mana

Sufeto janar na ‘yan sandan Najeriya, M.A Adamu ya shirya tsaf domin gabatar da wani taron kwana 3 domin horar da jami’an ‘yan sanda da kuma kara sanar da su a kan makamar aiki.

Wannan taro da aka sanya taken; “Yiwa hukumar ‘yan sanda kwaskwarima domin ta yi daidai da karni na 21” zai kasance ne daga ranar Litinin 28 zuwa Laraba 30 ga watan Oktoba a jihar Legas.

KU KARANTA: Tsige mataikamin Gwamnan Kogi abin kunya ne, PDP ta fadawa majalisar jihar Kogi

Har ila yau, wannan shirin na daya daga cikin yinkurin rundunar ‘yan sandan na ganin ta shigo da zamani cikin hanyoyin kawo tsaro a Najeriya.

A wani zancen da kakakin rundunar ‘yan sanda Najeriya, DCP Frank Mba ya fitarwa manema labari zaku ji cewa, Shugaba Muhammadu Buhari shi ne ya jagoranci bude taron.

Bugu da kari, zance ya sake sanar damu cewa, hukumonin tsaro daban-daban cikin har da na kasashen waje za su kasance a wurin taron.

Haka zalika, jami’an rundunar ‘yan sandan Najeriya manya daga cikinsu za su halarci taron daga jihohin kasar 36 da kuma birnin tarayya Abuja.

Mba ya ce: “A karshen wannan taro nana tsammanin jami’an ‘yan sandan za su karu da sanin hanyoyi daban-daban na magance matsalolin tsaro a zamanance.”

A wani labarin kuwa za ku ji cewa, hukumar daukar aikin ‘yan sanda wato Police Service Commission (PSC ta yi wani sauyi inda ta nada sabin mataimakan Sufeto janar wato DIG guda shida.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel