Zan kare 'yan Najeriya na gida da kasashen waje - Buhari

Zan kare 'yan Najeriya na gida da kasashen waje - Buhari

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bawa 'yan Najeriya da ke zaune cikin kasar da kasashen waje cewa gwamnatinsa za ta yi duk mai yiwuwa don ganin ta kare su.

Shugaba Buhari ya yi wannan jawabin ne a ranar Alhamis yayin da ya ke ganawa da dalibai da kwararru a birnin Sochi na kasar Rasha a cewar sanarwar da babban mai taimakawa shugaban kasa kan kafafen watsa labarai, Garba Shehu ya fitar.

Shugaban kasar ya yi alkawarin cewa gwamnatinsa za ta kare dukkan 'yan Najeriya ba tare da la'akari da nisarsu da gida ba kamar yadda The Cable ta ruwaito.

"Ran duk wani dan Najeriya a kowanne sashi na duniya yana da muhimmanci," a cewar shugaban kasar.

"Gwamnantin mu za ta kare 'yan Najeriya a gida da kuma na kasashen waje."

DUBA WANNAN: Bin diddigi: Shin gaskiya ne CIA ta yi hasashen cewa Najeriya za ta rushe kamar yadda Jega ya fadi?

Shugaban kasan ya yi bayyanin cewa an kafa Hukumar NIDCOM ne don amfanin amfanin 'yan Najeriya da ke kasashen waje da kula da tsaron su da kuma ba su damar bayar da gudunmawa domin ciyar da kasarsu gaba da iliminsu, kwarewarsu da arzikinsu.

Ya shawarci 'yan Najeriya da ke zama a kasashen waje su kasance masu bin doka da oda kuma su jajirce don ganin sunyi nasara a karatunsu ko ayyukan da suke yi.

Ya basu tabbacin cewa gwamnatinsa za ta rika bawa al'umma muhimmanci inda ya ce duk tsare-tsaren da gwamnatinsa ke yi na inganta tattalin arziki ne da tsare talakawa da al'umma masu rauni.

A wata rahoton, Legit.ng ta ruwaito cewa Shugaba Muhammadu Buhari ya baro kasar Rasha yana hanyarsa ta dawowa gida Najeriya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel