Yau kotu za ta raba gardama tsakanin Al-Makura da Adokwe

Yau kotu za ta raba gardama tsakanin Al-Makura da Adokwe

A yau, Juma'a 25 ga watan Oktoban 2015 ne kotun daukaka kara da ke Makurdi za ta yanke hukunci kan daukaka karar da Suleiman Adokwe ya yi na kallubalantar nasarar Sanata Umaru Tanko Al-Makura da wasu.

Sanata Adokwe ya kallubalanci nasarar Al-Makura a kotun kararrakin zabe amma bai samu nasara ba hakan ya sa ya daukaka kara zuwa kotun daukaka kara da ke Makurdi kuma kotun za ta yanke hukuncinta a yau kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

A ranar 30 ga watan Augustan 2019 ne kotun sauraron karrakin zabe da ke zamanta a Lafiya ta yi watsi da karar da jam'iyyar PDP da Suleiman Adokwe suka shigar na kallubalantar nasarar Sanata Tanko Al-Makura na jam'iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaben kujerar sanata na yankin Nasarawa ta Kudu.

DUBA WANNAN: Bin diddigi: Shin gaskiya ne CIA ta yi hasashen cewa Najeriya za ta rushe kamar yadda Jega ya fadi?

Kamfanin Dillancin Labarai na kasa (NAN) ta ruwaito cewa an yi zaben na a ranar 9 ga watan Maris na 2019 a gundumomi daban-daban da ke mazabar.

Adokwe, wanda ya yi sanata sai uku a jihar, ya kallubalanci nasarar Al-Makura kan cewa ba a gudanar da zaben kan dokokin zabe na 2010 ba.

Ya kuma yi ikirarin cewa an yi wa masu zabe barazana, an soke kuri'u ba bisa ka'ida ba tare da tafka magudi a zaben.

Sai dai alkalan kotun karkashin jagorancin Mai shari'a David Ugoh sun yanke hukuncin cewa wanda ya shigar da karar ya gaza gabatar da hujjoji gamsasu kan cewa anyi magudin zaben hakan yasa suka tabbatarwa Al-Makura nasara.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel