Zuwan Buhari Rasha zai gyara barnar da PDP ta yi na tsawon shekaru 16 - Princewill

Zuwan Buhari Rasha zai gyara barnar da PDP ta yi na tsawon shekaru 16 - Princewill

Wani tsohon dan takaran gwamna kuma mamba na kungiyar yakin neman zaben jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a jihar Rivers, Prince Tonye Princewill, ya mayar da martani ga wadanda ke korafi akan tafiye tafiyen diflomasiyya da Shugaban kasa Muhammadu Buhari ke yi.

Princewill ya bayyana wadannan tafiye-tafiyen musamman wanda Buhari ya yi kwanan nan zuwa Sochi a kasar Rasha a matsayin wajibi, don kau da makomar asaran da jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ta kawo wa kasar a tsawon shekaru 16 da tayi tana mulki.

A wani jawabin da ya gabatar a ranar Alhamis, 24 ga watan Oktoba, a Abuja, Princewill ya bayyana sakamakon tafiya zuwa Rasha da shugaban kasar ya yi a matsayin wani garabasa ga yan Najeriya, inda yake cewa yawan hannun jarin da ake zatton samu daga Rasha zai samar da dubban ayyuka, inda hakan ya nuna cewa Najeriya ta kasance zababbiyar masaukin zuba hannun jari.

KU KARANTA KUMA: Ya zama dole mataimakin gwamnan Kogi da aka tsige Achuba ya koma kujerarsa – Mambobin majalisar wakilai

Ya kara da cewa zuba hannun jarin Rasha zai kara daukaka martabar Najeriya kamar yanda yake a bayyane cewa hakan zai yi sanadiyyar bunkasa kasar.

Princewill yayi maganan yarjejeniya da dama hade da farfado da matatar man kasar, inganta tsarin tsaron Najeriya, kammala aikin kamfanin mulmula karfe na Ajaokuta da sauran su.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel