Ya zama dole mataimakin gwamnan Kogi da aka tsige Achuba ya koma kujerarsa – Mambobin majalisar wakilai

Ya zama dole mataimakin gwamnan Kogi da aka tsige Achuba ya koma kujerarsa – Mambobin majalisar wakilai

- Wani jigon majalisar wakilai na so a dawo da mataimakin gwamnan jihar Kogi da aka tsige, Simon Achuba

- Dan majalisar ya yi korafin cewa ba a bi ka’idojin da aka shimfida ba wajen tsige Achuba

- Yan majalisa a karkashin inuwar PDP na so majalisar dokokin tarayya ta dauki mataki cikin gaggawa

Mambobin majalisar wakilai a karkashin inuwar jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) sun bayyana tsige mataimakin gwamnan jihar Kogi, Simon Achuba a matsayin ba bisa ka’ida ba.

Kamfanin dillancin labaran Najeriya ta ruwaito cewa yan majalisar sun bayyana matsayarsu ne a wani jawabi dauke da sa hannun shugabansu, Kingsley Chinda daga jihar Rivers.

Mambobin majalisar wakilan sun bukaci majalisar dokokin kasar, kungiyoyin jama’a da yan Najeriya masu fada a ji da su dauki mataki domin kare damokradiyya daga durkushewa kwata-kwata.

KU KARANTA KUMA: Fashi da makami: Majalisa na so rundunar sojin sama ta gudanar da ayyukanta a Zamfara, Sokoto da Kebbi

Sun bayyana abunda ya kai ga tsige Achuba daga matsayinsa na mataimakin gwamna a matsayin tozarta kasar, inda suka ce ba a bi tsarin da ya kamata wajen tsige shi ba.

A baya Legit.ng ta rahoto cewa Jam’iyyar PDP reshen karamar hukumar Kabba ta jihar Kogi, ta bayyana tsige mataimakin gwamnan jihar Kogi da majalisar jihar tayi a matsayin abin kunya da kuma cin mutuncin dimokuradiyya.

A cikin wani zancen da ya samu sanya hannun Adebayo Kehinde, jam’iyyar ta ce sam bata ji dadin abinda majalisar dokokin tayi ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel