Da duminsa: Bayan ganawa da yan Najeriya mazauna Rasha, jirgi Buhari na hanyar dawowa gida (Hotuna)

Da duminsa: Bayan ganawa da yan Najeriya mazauna Rasha, jirgi Buhari na hanyar dawowa gida (Hotuna)

Jirgin shugaba Muhammadu Buhari AirForce 001 ya tashi daga filin jirgin saman Sochi domin dawowa gida Najeriya.

Gabanin tasowa, shugaba Buhari ya gana da kungiyar dalibai da ma'aikata yanNajeriya mazauna kasar Rasha a daren jiya.

Buhari ya tabbatarwa daliban cewa gwamnatinsa za ta kare mutuncin yan Najeriya a gida da waje.

Shugaba Muhammadu Buhari ya gana da shugaban kasar Rasha, Vladimir Putin kan abubuwa daban-daban na alfanu ga kasashen biyu.

Shugaba Buhari da Vladimir Putin sun a ranar Laraba a birnin Sochi sun yarde da cewa a gaggauta gudanar da ayyukan Rasha ta fara shekaru da yawa amma ba'a kammala ba har yanzu.

KU KARANTA: Yanzu-yanzu: An gurfanar da AbdulRashid Maina a kotu

Hakazalika shugabannin biyu sun amince da kaddamar da wasu sabbin ayyukan domin inganta kasuwanci, hannun jari, da tsaro.

Gabanin ganawarsu, Shugaba Muhammadu Buhari ya halarci taron gangamin shugabannin kasashen Afrika 30 da shugaban kasar Rasha, Vladimir Putin.

A taron kaddamarwan, Shugaba Putin ya ce kasar Rasha za ta ninka alakar kasuwancinta da Afrika cikin shekaru biyar masu zuwa.

Kalli hotunan:

Da duminsa: Bayan ganawa da yan Najeriya mazauna Rasha, jirgi Buhari na hanyar dawowa gida (Hotuna)
Da duminsa: Bayan ganawa da yan Najeriya mazauna Rasha, jirgi Buhari na hanyar dawowa gida (Hotuna)
Asali: Facebook

Da duminsa: Bayan ganawa da yan Najeriya mazauna Rasha, jirgi Buhari na hanyar dawowa gida (Hotuna)
Da duminsa
Asali: Facebook

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel