Yanzu-yanzu: An gurfanar da AbdulRashid Maina a kotu (Bidiyo)

Yanzu-yanzu: An gurfanar da AbdulRashid Maina a kotu (Bidiyo)

Tsohon shugaban kwamitin inganta kudin fansho, AbdulRashid Maina, ya dira babbar kotun tarayya dake Abuja yayinda hukumar hana almundahana da yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa wato EFCC ke gurfanar da shi.

Maina ya isa kotun ne tare da 'dansa, Farouq, wanda aka damkesu tare bayan yayi kokarin harbin jami'an DSS da bindiga.

Hukumar na zarginsa da laifin almundahanar kudaden yan fanshi N100 billion.

Babban kotun tarayya dake Abuja ta bada umurnin sadaukarwa gwamnatin tarayya dukiyoyi 23 da ake kyautata zaton na tsohon shugaban gyara harkan fansho, Abdulrashid Maina.

Alkali Folashade Ogunbanjo, ta bayyana umurnin ne ranar Talata yayinda take yanke hukunci kan karar da hukumar hana almundana da yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa wato EFCC.

A karar, hukumar yaki da rashawan ta bukaci kotun ta sadaukarwa gwamnati dukiyoyin dake da alaka da Maina.

A cewar EFCC, dukiyoyin da aka sadaukar na jihohin Kaduna, Borno, Sokoto da birnin tarayya Abuja.

Jerin dukiyoyin:

Yanzu-yanzu: An gurfanar da AbdulRashid Maina a kotu (Bidiyo)
Yanzu-yanzu: An gurfanar da AbdulRashid Maina a kotu (Bidiyo)
Asali: Facebook

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel