An yanke wa wani mai kula da makaranta shekara 60 a gidan maza kan yin zina da ‘yar shekara 2

An yanke wa wani mai kula da makaranta shekara 60 a gidan maza kan yin zina da ‘yar shekara 2

Justis Sybil Nwaka na kotun laifuka na musamman dake jihar Legas a ranar Alhamis, 24 ga watan Oktoba, ya yanke ma wani mai kula da makaranta, Adegboyega Adenekan hukuncin dauri na tsawon shekaru 60 a kurkuku bisa laifin yiwa daliba yar shekara biyu fyade.

An yanke ma Adenekan hukuncin ne bisa laifin yiwa dalibar makarantar Chrisland School, VGC fyade a cikin watan Nuwamba 2016.

A cewar lauyan mai karan, wanda ake zargin ya lalata dalibar ta hanyar saduwa da ita ba bisa doka ba.

A lokacin sauraron karan, mai gabatar da karan yayi kira ga shaidu bakwai sannan ya rufe karar a ranar 14 ga watan Maris, 2019, yayin da lauyoyin dake kare mai laifin ma suka kira shaidu biyar sannan suka rufe karansu a ranar 26 ga watan Yuni, 2019.

Yayin da take zartar da hukunci a ranar Alhamis, Justis Nwaka ta riki cewa mai gabatarwa ya bada shaida akan mai laifin fiye da zatto, inda ta kara da cewa shidar yarinyar da mai laifin yayi ma fyade sau biyu ya samu goyon baya daga sakamakon gwaji da cibiyar Mirabel, asibitin koyarwa na Jami’ar Jihar Legas dake Ikeja ta bayar.

KU KARANTA KUMA: Fashi da makami: Majalisa na so rundunar sojin sama ta gudanar da ayyukanta a Zamfara, Sokoto da Kebbi

da take bayar da shaida yarinyar tace jagoan makarantar ya sanya bakin shi da hannun shi a matancinta da na kawarta. Yarinyar ta ce a lokacin da ta so yin ihu sai mai laifin ya rufe mata baki.

Don haka mai shari'an ta yanke masa shekaru 60 a gia yari bayan tabbatar da hujjojin da aka gabatar a gabanta.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel