Fashi da makami: Majalisa na so rundunar sojin sama ta gudanar da ayyukanta a Zamfara, Sokoto da Kebbi

Fashi da makami: Majalisa na so rundunar sojin sama ta gudanar da ayyukanta a Zamfara, Sokoto da Kebbi

- Majalisar wakilai ta yi kira ga rundunar sojin saman Najeriya da su isar da aikinsu zuwa jihohin Zamfara, Sokoto da Kebbi saboda matsalolin tsaro da ake fuskata a chan

- Shugaban kwamitin majalisar wakilai akan sojin sama Mohammed Shehu Koko ne ya yi wannan kira a lokacin muhawarar kare kasafin kudin rundunar

- Ya ce kwamitin zai yi nazari akan kasafin kudin da rundunar sojin saman ta gabatar sannan ya yi gyare-gyare a inda ya kamata

Majalisar wakilai a jiya Alhamis,24 ga watan Oktoba, ta yi kira ga rundunar sojin saman Najeriya da su isar da aikinsu zuwa jihohin Zamfara, Sokoto da Kebbi saboda matsalolin tsaro da ake fuskata a chan.

Shugaban kwamitin majalisar wakilai akan sojin sama Mohammed Shehu Koko ne ya yi wannan kira a lokacin muhawarar kare kasafin kudin rundunar sojin sama.

Ya ce ya kamata rundunar sojin saman ta samar da jirgin daukar matakin gaggawa a jihar Kebbi domin kewaye yankin musamman cewa jihar na da iyakokin kasashen biyu na Benin da Nijar a cikinta.

KU KARANTA KUMA: Asiri ya tonu: Yadda aka kama fastoci biyu sunyi amfani da mace daya wajen nuna mu'ujizar karya (Bidiyo)

Ya kara da cewa kwamitin zai yi nazari akan kasafin kudin da rundunar sojin saman ta gabatar sannan ya yi gyare-gyare a inda ya kamata domin ya isar da hakkin kundin tsarin mulki da ya rataya a wuyan shi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel