Yadda wani ma’aikaci ya kona ofishinsa bayan ya yi awon gaba da N1.4m

Yadda wani ma’aikaci ya kona ofishinsa bayan ya yi awon gaba da N1.4m

Katankatana, wani babban ma’aikacin kamfanin sarrafa abinci na Sweet Sensation, kuma jami’in kula da asusun kamfanin, Mista Michael Thadius ya yi awon gaba da kimanin N1,400,000 daga asusun kamfanin sa’annan ya banka ma ofishin nasa wuta, ya buga ma wandonsa iska.

Kamfanin dillancin labaru, NAN, ta ruwaito jami’in rundunar Yansandan Najeriya reshen jahar Legas mai shigar da kara, Sajan Felicia Okwori ce ta bayyana haka ga Alkalin kotun majistri dake zamanta a Ikejan jahar Legas.

KU KARANTA: A Zango ya raba guraben tallafin karatu ga fadar Sarkin Zazzau, APC da PDP

Yarsandan ta bayyana cewa suna tuhumar Thadius da aikata laifin kunna wuta a ofis, barazanar janyi asara, sata da kuma kokarin tayar da gobara, sai dai Thadius ya musanta dukkanin tuhume tuhumen nan.

Yarsandan ta bayyana cewa Thadius ya tafka wannan laifi ne a ranar 25 ga watan Satumba a ofishin kamfanin Sweet Sensation dake kan layin Olowora, yankin Ojudu Berger na jahar Legas, inda ya sace N1.4m, sa’annan ya banka ma ofishinsa wuta.

A cewar Yarsanda Felicia, laifin ya saba ma sashi na 343, 342, 344 da kuma 287 na kundin hukuncin manyan laifuka na jahar Legas wanda suka tanadi hukuncin daurin rai da rai idan har aka kama mutum da laifi.

Sai dai a sakamakon musanta tuhume tuhumen, Alkalin kotun, G.O Anifowoshe ya bada belin Thadius a kan kudi N100,000 da mutane biyu da zasu tsaya masa a kan nara dubu dari dari, wanda dole su kasance masu aikin yi, kuma su bayyana shaidar biyan haraji ga gwamnatin jahar Legas na tsawon shekaru biyu.

Daga karshe Alkali G.O ya dage cigaba da sauraron karar zuwa ranar 20 ga watan Nuwamba.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel