An kama wata Uwa da ya’ay’anta 3 da laifin sha da sayar da barasa a Zamfara

An kama wata Uwa da ya’ay’anta 3 da laifin sha da sayar da barasa a Zamfara

Hukumar kula da dokokin shari’ar musulunci ta kama wasu mutane uku da hannu dumu dumu cikin yin karantsaye ga dokar da ta haramta sha da cinikin giya ko barasa a jahar Zamfara, inji rahoton kamfanin dillancin labaru, NAN.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito hukumar ta kama mutanen su uku ne a unguwar Tudun Wada dake cikin garin Gusau na jahar Zamfara, kamar yadda shugabanta, Dakta AAtiku Zawiyya ya bayyana.

KU KARANTA: A Zango ya raba guraben tallafin karatu ga fadar Sarkin Zazzau, APC da PDP

Zawiyya ya bayyana haka ne yayin da yake bayyana mutanen ga manema labaru a babban ofishin hukumar dake garin Gusau a ranar Alhamis, 24 ga watan Oktoba, inda yace sun samu nasarar kamasu ne bayan samu tare da tattara bayanan sirri daga hannun wasu matasan unguwar.

Zawiyya yace jami’an hukumarsa sun kama wata mata mai suna Madam Mariam, Lydia Samuel da kuma John Samuel ne a gidansu tare da kwalaben giday guda 103 da kuma jarkoki guda biyu cike fal da barasa.

Babban sakataren hukumar shari’ar musuluncin ya cigaba da cewa har yanzu suna cigaba da gudanar da bincike a kan lamarin, kuma da zarar sun kammala zasu gurfanar dasu gaban kuliya manta sabo domin fuskantar hukunci.

Daga karshe Zawiyya ya bayyana cewa doka ta basu daman kamawa, bincike tare da gurfanar da mai laifi gaban kotu, don haka ya yi kira ga jama’a dasu dinga basu ingantattun bayanan sirri game da masu aikata miyagun laifuka a jahar.

Haka zalika shugaban ya nemi gwamnatin jahar ta kara kaimi wajen baiwa hukumar tallafin kayan aiki da ababen sufuri domin ta ji dadin gudanar da aikinta tare da sauke nauyin daya rataya a wuyarta cikin sauki.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel