Na yi wa 'ya'ya na biyu fyade ne don gwada kuzari na - Mahaifi

Na yi wa 'ya'ya na biyu fyade ne don gwada kuzari na - Mahaifi

'Yan sanda a jihar Akwa Ibom sun kama wani Joseph Sunday da ya yi wa 'ya'yan cikinsa masu shekaru 9 da 13 fyade.

Wanda ake zargin dan asalin garin Obot Ideng a karamar hukumar Ibesikpo ya fara lalata da 'ya'yansa ne shekaru uku da suka gabata bayan sun rabu da matarsa. Rahotanni sun ce mahaifiyar yaran tana zama a jihar Rivers.

Bincike ya nuna cewa Mista Sunday da ake kyautata zaton ya kusa kai shekaru 50 ya kan yi lalata da 'ya'yansa mata biyun a lokaci guda a gidansa da ke Ibesikpo.

An kuma bayyana cewa wanda ake zargin ya yi wa 'ya'yan sa barazana da wani maganin gargajiya (mbiam) idan suka sake suka fada wa wani abinda ke faruwa tsakaninsu.

DUBA WANNAN: Ministan Buhari ya mayar da wasu makuden kudi da aka tura wa ma'aikatansa kan kuskure

Amma asirinsa ya tonu bayan ya kama 'yarsa mai shekaru 13 tare da wani mutum da ya ce shi saurayinta ne kuma ya yi yunkurin ladabtar da ita.

Bacin rai ya saka shi dukan 'yarsa hakan kuma ya saka ta tona asirin mahaifin na ta.

Dayan 'yarsa mai shekaru tara ita ma ta bayyana cewa mahaifinta na lalata da ita kuma ta ce tana son kaunarsa kana tana jin dadin abinda ke faruwa tsakaninsu.

Mista Sunday ya amsa cewa yana lalata da 'ya'yansa inda ya ce yana son ya rika gwaji ne don ya tabbatar da karfinsa a matsayin da na miji.

Ya ce, "Mun rabu da mata ta saboda wasu matsaloli na gida shekaru kadan da suka shude. Ni kadai na ke kulawa da 'ya'ya na. Kawai ina son in tabbatar cewa ina nan da karfi na a matsayin na miji ne shi yasa na ke amfani da 'ya'ya na."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel