Yanzu - Yanzu: An kara bankado wani gidan kangararru a jihar Kwara

Yanzu - Yanzu: An kara bankado wani gidan kangararru a jihar Kwara

- A kalla mutane 108 ne aka tseratar daga wani gidan kangararru a jihar Kwara

- Wadanda aka tseratar din sun bayyana cewa, iyayensu sun kaisu don gyaran hali ne sabanin abinda ke faruwa a gidan

- A cikin kwanakin nan ne aka bankado gidajen horarwa masu yawa a arewacin kasar nan

A kalla mutane 108 ne aka tseratar daga wani gidan kangararru a jihar Kwara.

Wadanda aka tseratar din sun yi ikirarin cewa, iyayensu sun kaisu ne don gyaran hali wanda a maimakon hakan ne ake azabtar dasu tare da muzguna musu.

Wasu daga cikinsu sun ce, iyayensu sun biya daga naira dubu dari zuwa dubu dari biyu don a gyara musu dabi’u.

KU KARANTA: Dalilin da yasa jaruma Hafsat Idris ta fashe da kuka yayin wani taro

A cikin kwanakin nan ne ake ta bankado gidajen horarwa a jihohi daban-daban na arewacin Najeriya.

An fara bankado gidan horarwa ne a jihar Kaduna inda ake azabtar da daliban tare da koya musu karatu. Amma duba da irin azabar da suke fuskanta ta sha gaban yawan karatun da ake basu, yasa gwamnatin tarayya ta bukaci a rufe gidan.

An cigaba da bankado gidajen horarwar ne jihar Katsina da wasu kuma a jihar Kaduna. Kwatsam kuma sai gashi a jihar kwara a yau.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel