Hukumar NEMA ta kai agaji ga mutanen da yan bindiga suka tarwatsa a Kaduna

Hukumar NEMA ta kai agaji ga mutanen da yan bindiga suka tarwatsa a Kaduna

Hukumar bada agajin gaggawa ta Najeriya, NEMA ta bayyana cewa mutane 5 ne suka mutu a sanadiyyar harin da wasu gungun miyagu yan bindiga suka kai cikin karamar hukumar Igabi ta jahar Kaduna a yan kwanakin nan.

Rahoton kamfanin dillancin labarun Najeriya, NAN, ta bayyana hukumar ta NEMA tana cewa yan bindigan da suka kai wannan hari sun tashi kauyuka guda 17 dake cikin karamar hukumar Igabi, tare da jikkata mutane biyu.

KU KARANTA: Kungiyar Boko Haram ta samu karin mayaka 2000 daga ISIS – Shugaban kasar Rasha

Shugaban hukumar na shiyyar Arewa, Ishaya Chinoko ne ya bayyana haka a ranar Alhamis, 24 ga watan Oktoba yayin da ya kai ziyarar gani da ido zuwa wata makarantar firamari ta LEA Birnin Yero inda mutanen kauyukan suka taru suna gudun hijira.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Mista Ishaya yana cewa ya kai wannan ziyara ne domin gane ma idanunsa halin da jama’an suke ciki, tare da sanin adadinsu domin sanin iya kayan tallafin da zasu kai musu.

Ya kara da cewa a yayin wannan ziyarar daya kai ma jama’an ne suka sanar dashi cewa yan bindigan sun kashe mutane biyar a sakamakon harin da suka kaddamar, da kuma mutane biyu da suka samu rauni.

Daga karshe Ishaya ya jajanta ma gwamnati da al’ummar jahar Kaduna, sa’annan ya basu tabbacin mika rahoton bayanan da ya samu a yayin wannan ziyara ga shugabancin hukumar NEMA domin samo musu tallafi daga gwamnatin tarayya.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel