Neman haramta siyar da barasa da shan sa ya haifar da tashin hankali a Zaria

Neman haramta siyar da barasa da shan sa ya haifar da tashin hankali a Zaria

Hankula sun tashi a Karamar hukumar Sabon Gari, Zaria a ranar Alhamis, 24 ga watan Oktoba, a wajen sauraron dokar da ake neman kafawa na haramta siyarwa da kuma shan barasa da sauran kayan maye a hukumar.

A wata wasika mai dauke da kwanan wata 21 ga watan Oktoba, 2019, an gayyaci kungiyar masu otel da wajen siyar da barasa domin sauraron shari’an.

Da suke bayyana ra’ayinsu a wajen zaman ta hannun lauyansu, Mista Daniel Peters, sun bayyana cewa karamar hukuma a Najeriya na da ikon bayar da Lasisi, takaitawa da kuma kula da siyar da kayan maye, basu da ikon haramta siyar da kayan barasa haka kuma basu da karfin hana shan barasa.

Haka zalika da yake ingiza neman dakatar da dokar a zaman, wani mai siyar da barasa na gargajiya wanda aka fi sani da burkutu, Richard Sankai ya bayyana cewa siyar da barasar na taimakawa zawaran da mazajensu suka mutu wajen kula da iyalinsu.

KU KARANTA KUMA: Shakka babu Adam Zango ya biya N46m domin karatun marayu – Shugaban makarantar Professor Ango Abdullahi

A halin da ake ciki, kungiyar Jama’atu Nasril Islam (JNI) da kungiyar Kiristocin Najeriya (CAN) a Zaria sunce babu addinin da goyi baya ko yayi kira ga sha da siyar da barasa.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel