Matashi ya mutu a watan da ya samu aiki bayan shafe shekaru 6 yana neman aiki

Matashi ya mutu a watan da ya samu aiki bayan shafe shekaru 6 yana neman aiki

Wani matashi da ya shafe shekaru shidda yana neman aiki ya mutu ana saura kwana daya a biya shi alfashi na farko a aikin da ya samu.

Matashin, Sylvanus Okpanachi, ya kammala karatu a wata babbar makaranta a shekarar 2013 amma bai samu aiki ba sai bayan shekaru shidda.

Rahotanni sun bayyana cewa matashin ya mutu ne sakamakon wani hatsarin mota da ya ritsa da shi ranar Lahadi, 21 ga watan Oktoba, a lokacin da ake tsammanin zai fara karbar albashinsa na farko a ranar Litinin, 22 ga watan Oktoba.

Wani abokin matashin da suka hadu ranar Juma'a ne ya sanar da labarin mutuwar, tare da bayyana cewa marigayin ya fada masa cewa ranar Litinin zai karbi albashinsa na farko bayan samun aikin da ya shafe shekaru shidda yana nema.

Asali: Legit.ng

Online view pixel