Ministan Buhari ya yiwa 'yan Najeriya tallar guraben aiyuka a kasashen ketare

Ministan Buhari ya yiwa 'yan Najeriya tallar guraben aiyuka a kasashen ketare

- Ma'aikatar jharkokin kasashen waje ta taya wasu kasashe biyu tallar guraben aiyuka

- Cibiyoyi biyu ne amma duk namusulunci a kasashen Morocco da Kazakhstan suke bukatar ma'aikata

- Kasar ta Najeriya ta jawo hankulan masu neman aiyuka ko zasu gwada sa'arsu

Ma’aikatar harkokin waje ta yi tallar guraben aiyuka a madadin kasashen Morocco da Kazakhstan.

Cibiyar habaka kasuwanci ta addinin musulunci ta kasar Morocco da kungiyar tsaro ta abinci ta Kazakhstan, sun yi tallar guraben aiyuka a kasashensu. A don haka ne ma’aikatar harkokin kasashen waje ta Najeriya ta jawo hankulan ‘yan kasar don gwada sa’arsu.

Dama dai rashin aikin yi yayi katutu a kasar Najeriya. A ra'ayin wasu mutane, hakan kuwa shi ke kawo karuwar yawan aika-aikar da ke faruwa a kasar.

KU KARANTA: Malami ya bukaci 2.5% na kudin Abacha don amfanin ofishinsa

Ma’aikatar ta yi amfani da shafinta na tuwita ne don sanarwar.

Mutanen da yawa da suka maida martani akan rubutun sun nuna damuwarsu ne saboda ba basu iya yaren larabci ba kuma ba musulmai bane.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel