Jerin sunaye: NJC ta amince da nadin sabbin alkalan kotun koli 4

Jerin sunaye: NJC ta amince da nadin sabbin alkalan kotun koli 4

Majalisar Kolin Alkalan Najeriya, NJC ta zabi mutane hudu da ke son a nada a matsayin sabbin alkalaia kotun koli.

Sanarwar neman nadin ta fito ne daga bakin direkatan yadda labarai na NJC, Soji Oye, Esq a ranar Alhamis 24 ga watan Oktoban 2019.

Wadanda aka za a yi wa nadin su ne:

1. Hon. Justice Adamu Jauro (Yankin Arewa maso Gabas)

2. Hon. Justice Emmanuel A. Agim, (Yankin Kudu maso Kudu)

3. Hon Justice C. Oseji, JCA (Yankin Kudu maso Kudu)

4. Hon Justice Helen M. Ogunwumiju, (Yankin Kudu maso Yamma)

DUBA WANNAN: An bankado wani gidan da 'yan mata masu kananan shekaru ke haihuwa don safarar jariran

An aikewa Shugaban kasa Muhammadu Buhari sunayen su domin shi ke da ikon nada alkalan tare da amincewar Majalisar Dattawa.

Har ila yau, NJC ta kuma bukaci a nada wasu jami'an ma'aikatan shari'ar 13 a manyan kotunan tarayya da jihohi kamar yadda ya ke cikin sanarwar ta majalisar ta fitar.

Alkalan sun fito ne daga sassan Najeriya daban-daban kuma za a nada wasu daga cikinsu a matsayin alkalan kotunnan tarayya yayin da wasu kuma alkalan kotunan jihohi.

Ana sa ran dukkan za a rantsar da dukkan alkalan da aka zaba bayan Shugaban kasa da Gwamnonin jihohinsu da Majalisar Dattawa da ta jihohi sun amince da su.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel