Dalilin da yasa ta'addanci ya ki ci ya ki cinye wa a Najeriya - ICMC

Dalilin da yasa ta'addanci ya ki ci ya ki cinye wa a Najeriya - ICMC

Rashin shugabanni masu son kawo canji ne dalilin da yasa har yanzu ake fama da kallubalen rashin tsaro a Najeriya a cewa Cibiyar Koyar da Kwararrun Masu Sulhu (ICMC) kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Rajistaran cibiyar, Segun Ogunyannwo ne ya bayyana hakan yayin da ya ke magana da manema labarai a wurin taron kwana daya kan salon shugabanci na kawo canji da aka shirya don tunkarar kallubalen tsaro don hukumomin tsaro, kafafen watsa labarai da kungiyoyin inganta rayuwar al'umma a ranar Alhamis a Abuja.

Ya ce, "Idan za a yi wa hukumomin tsaro adalci, suna iya kokarin su. Babban kallubalen da muke fama da ita a wannan kasar shine na shugabanci.

"Muna da shugaban karamar hukuma da ya kamata ya zama babban jami'in tsaro na karamar hukumarsa amma ba shi da iko kan wadanda ya kamata su samar da tsaron.

DUBA WANNAN: An bankado wani gidan da 'yan mata masu kananan shekaru ke haihuwa don safarar jariran

"Akwai karancin shugabanci na gari a kasar nan. Shugabanin mu a kasar nan suna yawa da jami'an tsaro masu yawa a kasar da dan sanda guda ne zai samarwa mutane 5,000 tsaro.

"Hakan na nuna cewa ba talakawa su ke yi wa hidima ba, kan su suke yi wa hidimar."

Ya kara jadada cewa abinda Najeriya ke bukata shine 'shugabanni marasa son kai, wadanda suke son yin shugabanci da zai samar da tsaro ga dukkan al'umma ba wai kansu kadai ba.

A bangarensa, wanda ya shirya taron kara wa juna ilimin tare da hadin gwiwan NSCDC, Lord James Okpanachi ya ce an shirya taron ne domin samar da canji dabarun samar da tsaro a Najeriya.

Ya ce, "Muna kokarin nemo wasu dabaru ne tunda ba wanda zai iya aiwatar da tsare-tsare ba tare da hadin kan shugabanni ba.

"Akwai alaka tsakanin shugabanci da rashin tsaro kuma a tunanin mu duk shugaban da ba zai iya kawo canji ba ya kamata shi a canja shi."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel