Shakka babu Adam Zango ya biya N46m domin karatun marayu – Shugaban makarantar Professor Ango Abdullahi

Shakka babu Adam Zango ya biya N46m domin karatun marayu – Shugaban makarantar Professor Ango Abdullahi

Shugaban makarantar Professor Ango Abdullahi da ke Zariya, Dr Shamsuddeen Aliyu Maiyasin, ya ce babu tabbatar da batun biyan naira miliyan 46 da fitaccen jarumin nan, Adam Zango ya zuba a makarantar domin daukar nauyin karatun yara marayu su 101.

Dr Shamsuddeen ya kara da cewa ba wannan ne karon farko ba da fitaccen jarumin yake bayar da irin wannan gudunmawa ba ga marasa karfi musamman kan abin da ya shafi karatunsu.

Ga cikakken jawabin nasa: “Wato Professor Ango Abdullahi makaranta na ne, akwai makarantunmu muna da daya group of day school, muna kiranta da Professor Ango Abdullahi group of school anan zaria, toh karkashinta akwai wasu makarantu irinsu Professor Ango Abdullahi Int’l School, irin su mallawa int’i school suna nan da yawa wanda dukkansu suna karkashin professor int group of

“Gaskiyar magana da gaske ne shi Adam A zango ya jima yana daukar nauyin dalibai a sanina ba ma a nan makarantar namu ba kawai. Akwai wasu makarantu da ya sha daukar nauyin dalibai harma na gaba da sakandare.

“Ya ma taba daukar nauyin wasu yara wadanda suka tafi sangaya sudan wanda nine nayi masu hanya aka dai turasu, toh amma shi damuwarsa baya so asan ya yi , yana ta boyewa, toh ko wannan karan da aka yi lissafi zai biyawa yara 101 kudi lura da yadda yara marayu ke zama lalatattu suna komawa shaye-shaye wasu ma suna rikidewa suna zama yan kidnapping da dai sauransu shine yace yana so ya taimaki yaran nan maayu amma matasa, shine aka dauki yara wadanda suka gama Jss za su tafi SS su 101 aka biya kudinsu aka yi lissafi karkashin professor int group of school.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Najeriya za ta siyi helikoftan kai hari 12 daga Rasha bayan yarjejeniyar soji

“An saka kudinsu a gidauniyar farfesa abdullahi dake nan cikin birnin zaria, nine nace lallai sai an yada abun saboda bai kamata ace mutum na irin wannan kokarin sannan kuma ace sai an boye ba kamar yadda yake yi a chan baya.

“Kamar a baya akwai wasu yara dake karatu tare da yayansa sun fara karatun sai iyayensu suka mutu sai yace kada a cire su shi zai cigaba da biya masu kudin makaranta.”

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel