Tsige mataikamin Gwamnan Kogi abin kunya ne, PDP ta fadawa majalisar jihar Kogi

Tsige mataikamin Gwamnan Kogi abin kunya ne, PDP ta fadawa majalisar jihar Kogi

Jam’iyyar PDP reshen karamar hukumar Kabba ta jihar Kogi, ta bayyana tsige mataimakin gwamnan jihar Kogi da majalisar jihar tayi a matsayin abin kunya da kuma cin mutuncin dimokuradiyya.

A cikin wani zancen da ya samu sanya hannun Adebayo Kehinde, jam’iyyar ta ce sam bata ji dadin abinda majalisar dokokin tayi ba.

KU KARANTA:Ministan sadarwa ya dau wani mataki na musamman ga kamfanonin sadarwar wayar hannu

Jam’iyyar ta PDP ta ce: “Abin takaicine ganin cewa daya daga cikin sassan gwamnati dake da ikon amfani da kundin tsarin dokokin kasa domin yanke huknci, ya tsaya jiran umarni daga majalisar zartarwa.

“Wannan fashi da makami ne aka yiwa dimokuradiyya da kundin tsarin mulkin Najeriya a majalisar jihar Kogi. Cire Simon Achuba sam bai da ce da dokar kasa ba.” Inji PDP.

Adebayo yayi magana mai tsawo game da tsige Simon daga bisa kujerarsa ta mataimakin gwamnan jihar Kogi, inda yake cewa duk da kwamitin binciken sun tambara wadansu laifuka guda shida a kansa amma hakan bai isa hujjar cewa a cire shi ba.

Ya kuma kara da cewa, Kakakin majalisar jihar, Mathew Kolawole ya ba shi kunya kasancewar ya aikata abinda ya sabawa kundin tsarin mulkin Najeriya wanda ko wace majalisa ke amfani da shi wurin yanke hukunci.

A wani labarin kuwa zaku ji cewa, Ministan sadarwa, Dr Isa Ali Pantami ya umarci NCC da ta hukunta duk kamfanin sadarwar da aka samu da laifin cire kudin USSD ga masu aiki da layinsu.

Uwa Suleiman, mai magana da yawun bakin ministan ce ta fitar da wannan a ranar Alhamis 24 ga watan Oktoba, 2019 a cikin wani zancen da ta bai wa ‘yan jarida.

https://www.sunnewsonline.com/pdp-to-kogi-assembly-your-impeachment-of-dep-gov-shameful-threat-to-democracy/

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel