Zai fi kyau idan Gwamnati ta bude kan iyakar Najeriya, inji wani babban lauya

Zai fi kyau idan Gwamnati ta bude kan iyakar Najeriya, inji wani babban lauya

Babban lauyan nan mai fafutukar kare hakkin bil adama, Femi Falana (SAN) ya ba gwamnatin tarayya shawarar ta bude kan iyakan kasar saboda maslaharta.

Falana ya ce bude kan iyakar yana tattare da wani alfanu mai girma ga gwamnatin Najeriya. A cewarsa, a maimakon rufe kan iyakar, kamata yayi Najeriya ta zauna da kasashen dake makwabtaka da ita domin magance matsalar fasa kwaurin makamai.

KU KARANTA:Ministan sadarwa ya dau wani mataki na musamman ga kamfanonin sadarwar wayar hannu

Kwararren lauyan ya yi wannan maganar ne ranar Alhamis 24 ga watan Oktoba, 2019 a birnin Accra dake Ghana inda ya halarci wani taron kungiyar ECOWAS.

Falana ya yi kira ga gwamnatin Najeriya da cewa ta manta da maganar IMF na goyon bayan rufe kan iyakar da ta yi. Inda ya ce: “IMF din tayi hakan ne da gan-gan domin ta durkushe kungiyar ECOWAS da hadin kan yankinta gaba daya.”

Har ila yau, Falana yayi magana mai tsawo game da rufe kan iyakar Najeriya, inda yake cewa ko kadan bai kamata a ce Najeriya ta biyewa IMF ba.

Ya kara da cewa, rashin fa’idar rufe kan iyakar nan yafi yawa idan aka kwatanta shi da fa’idar rufewar. Ya ce za a iya zama tsakanin Najeriya da kasashen dake makwabtaka da ita domin dinke bakin matsalar dake aukuwa a kan iyakar.

A karshe ya umarci gwamnatin Najeriya da ta bude kan iyakar nata cikin gaggawa domin samun alfanu a bangaren tattalin arziki da ma wasu abubuwan da dama.

https://punchng.com/end-border-closure-in-national-interest-falana-advises-fg/

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel